IQNA

Najeriya: Gwamnatin Jihar Kwara Ta Bayar Da Izin Saka Hijabi A Makarantun Jihar

20:19 - February 26, 2021
Lambar Labari: 3485691
Tehran (IQNA) gwamnatin jihar Kwara a Najeriya ta bayar da izinin saka hijabin musulunci ga dalibai mata musulmi da suke bukatar hakan.

Shafin yada labarai na all Africa ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin jihar Kwara da ke tarayyar Najeriya ta bayar da izinin saka hijabin musulunci a hukumance ga dukkanin dalibai mata musulmi da suke bukatar yin hakan a cikin makarantun da ke fadin jihar.

Baya ga haka kuma gwamnatin jihar Kwara ta sanar da sake bube wasu makarantu guda 10 da aka rufe a birnin Ilorin fadar mulkin jihar, sakamakon wasu batutuwa da suka taso da suka shafi batun saka hijabi.

A cikin bayanin da gwamnatin Jihar Kwara ta fitar, ta bayyana cewa daukar wannan mataki shi ne yafi zama maslaha, domin kuwa akwai bukatar hadin kai da fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya addinai na musulunci da kiristoci a jihar, kuma an dauki wannan matakin ne bayan tuntubar dukkanin bangarorin biyu.

Haka nan kuma an kirayi dukkanin jagorori na musulmi da kirista da kuma masana daga bangarorin biyu, da su bayar da dukkanin gudunmawa da zata taimaka wajen samun sulhu da dawwamamen zaman lafiya a Najeriya baki daya.

 

3956333

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha