IQNA

20:24 - February 26, 2021
Lambar Labari: 3485693
Tehran (IQNA) yahudawan sahyuniya sun hana musulmi gudanar da sallar Juma'a a yau a cikin masallacin aqsa mai alfarma.

Shafin yada labarai na WAFA ya bayar da rahoton cewa, a yau jami'an tsaron gwamnatin yahudawan Isra'ila  sun hana musulmi gudanar da sallar Juma'a cikin masallacin aqsa mai alfarma, kamar yadda sukan yi lokaci zuwa lokaci.

Hafzi Abu Sanina, mai kula da harkokin masallacin aqsa ya bayyana cewa, tun a jiya Alhamis, jami'an tsaron yahudawan dauke da makamai suka shiga cikin harabar masallacin mai afarma.

Ya ce sun hana gudanar da kiran sallar la'asar tun daga jiya, sun kuma ba za a sake yin kiran salla a cikin masallacin quds ba har zuwa ranar Lahadi, saboda gobe Asabar ranar idin Purim ce, daya daga cikin ranakun idin yahudawa.

Abu Sanina ya ce, a yau kuma sun hana musulmi shiga cikin masallacin domin gudanar da sallar Juma'a, baya ga haka ma sun kame wasu daga cikin musulmi Falastinawa da suka yi yunkurin shiga cikin masallacin.

3956375

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ، ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: