IQNA

21:49 - February 27, 2021
Lambar Labari: 3485697
Tehran (IQNA) 'yan majalisar dokokin Amurka 140 daga jam'iyyar Democrat sun bukaci a soke dokar hana musulmi shiga Amurka daga wasu kasashe.

Rahotanni daga Amurka sun ce 'yan majalisar dokokin kasar ta Amurka 140 daga jam'iyyar Democrat sun bukaci a soke dokar hana musulmi shiga kasar daga wasu kasashen musulmi da na larabawa, da kuma wasu kasashen da ba su dasawa da gwamnatin Amurka.

An kafa wannan doka ne a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar ta Amurka Donald Trump, wanda ya kafa dokar da nufin cin zarafin musulmi da kuma mayar da su saniyar ware a cikin kasar ta Amurka, da kuma kara ruruta wutar kiyayya da kin jini a kansu.

Kasashen da dokar ta shafa dai sun hada da Iran, Syria, Libya , Yemen, Somalia, sai kuma wasu daga cikin kasashen da ba su shri da Amurka, da suka hada da Koriya ta arewa da kuma Venezuela.

'Yan majalisar sun yaba wa Joe Biden kan janye dokar da ya yi a tashin farko bayan karbar ragamar shugabancin kasar Amurka, amma sun bayyana cewa abin bukata shi ne a soke dokar kwata-kwata tare da haramta ta, domin kuwa wasu shugabanni za su iya dawo da ita a wasu lokuta masu zuwa.

Ilhan Omar 'yar majalisar dokokin Amurka musulma ta bayyana cewa, babbar manufar kafa wannan doka da Trump ya yi ita ce take hakkokin musulmi na addini, tare da kokarin ingiza Amurkawa da su kyamace su.

 

3956431

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: