IQNA

Paparoma Francis: Ziyarata A Iraki Tana Nan Daram

23:47 - March 04, 2021
Lambar Labari: 3485713
Tehran (IQNA) babban jagoran mabiya addinin kirista na darikar Katolika Paparoma Francis ya bayyana cewa ziyarar da yake shirin kaiwa a Iraki tana nan daram.

A cikin rahoton da shafin yada labarai na Mawazin News ya bayar ya bayyana cewa, a cikin bayanin da fadar Vatican ta fitar, babban jagoran mabiya addinin kirista na darikar Katolika Paparoma Francis ya bayyana cewa ziyarar da yake shirin kaiwa a Iraki tana nan kamar yadda aka tsara.

Bayanin ya ce, za a rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi, da suka hada da wajabcin girmama juna da ‘yan uwantaka tsakanin ‘yan adam, da kuma yin Allawadai da duk wani nau’in ta’addanci a kan ‘yan adam, da kuma karfafa tattaunawa tsakanin addinai na duniya, musamman kiristanci da muslunci.

Ziyarar Paparoma a Iraki za ta fara ne a  ranar 5 ga watan Maris mai kamawa, inda zai samu taba daga firayi ministan Iraki Mustafa Alkazimi a filin sauka da tahsin jiragen sama na Bagdad, daga nan kuma zai nufi fadar shugaban kasar Iraki, inda zai gana da shugaban kasar Barham Saleh, da kuam wasu manyan jagororin mabiya addinin kirista, da kuma ziyartar wasu majami’oi.

A ranar 6 ga wata kuma zai nufi birnin Najaf, inda zai gana da Ayatollah Sayyid Ali Sistani, daga nan kuma zai wuce zuwa lardin Ziqar, inda zai ziyarci yankin da aka haifi annabi Ibrahim (AS) bayanan kuma a ranar 7 ga wata zai isa birnin Arbil, daga nan kuma zuwa Mosil inda zai ziyarci majami’ar kiristoci ta tarihi.

3957497

 

 

 

captcha