IQNA

22:05 - March 05, 2021
Lambar Labari: 3485716
Tehran (IQNA) an samar da wasu nau’in kaya na musamman masu sututa jiki ga jami’an tsaro mata musulmi a birnin Leicester na kasar  Burtaniya.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, an samar da wasu nau’in kaya na musamman masu sututa jiki ga jami’an tsaro mata musulmi a birnin Leicester na kasar  Burtaniya, wanda a halin yanzu mata jami’an tsaro musulmi suke yin amfani da shi a birnin, kafin daga bisani kuma a rika amfani da shi a kasar baki daya.

Wannan nau’in tufafi yana da tsari na musamman da zai taimaka ma mata musulmi a lokacin da suke gudanar da aikinsu, baya ga cewa ya rufe jikinsu, a lokaci guda kuma an yi kayan suna damfare da juna sosai, ta yadda lullubin da ke kansu ba zai fita a lokacin da suke kokarin kama mai laifi.

Rahoton na Aljazeera ya kara da cewa, ko babu komai hakan babban ci gaba ne, domin ya tabbatar da cewa an amince da akidar musulunci ta saka lullubi ga mata da kuma suturta jikinsu, wanda hakan zai baiwa mata musulmi jami’an tsaro damar gudanar da aikinsu cikin natsuwa.

3957580

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: