IQNA

Iran Ta Mayar Da Kakkausan Martani Kan Bayanin Bayan Taron Kasashen Larabawa

21:33 - March 06, 2021
Lambar Labari: 3485718
Tehran (IQNA) Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta mayar da martani dangane da bayanin bayan taron kasashen larabawa, da ke  zarginta da yin kutse a cikin harkokin kasashen yankin.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatib Zadeh ya bayyana cewa, dukkanin abin da ya zo a cikin bayanin bayan taron kasashen larabawan babu sabo a cikinsa, abin da suka saba yi ne idan sun gama su waste.

Ya ce abin ban takaici ne yadda kungiyar kasashen larabawan ta zama ba ta da wani katabus, kuma ba za ta iya zartar da komai ba sai abin da wasu ‘yan tsiraru daga cikin gwamnatocin larabawa suke bukata.

Dangane da zargin da ya zo cikin bayanin bayan taron na kasashen larabawa da ke cewa Iran ce ke da hannu a matsalolin da kasashen larabawan yankin suke fuskanta, Saeed Zadeh ya bayyana hakan da cewa shi kansa wani nau’i ne na wawantar da sauran kasashen da ke halartar taron da ma sauran kasashen duniya.

Ya kara da cewa, kasashen da suke kafa alka’ida da Daesh da sauran kungiyoyin ‘yan ta’addan takfir da ke yi wa ‘yan adam yankan rago da tayar da bama-bamaia  cikin masallatai da kasuwanni, su ne suke zargin Iran da goyon bayan ta’addanci.

Haka nan uma ya yi ishara da kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar kasashen Yemen, inda masu yin kisan gilla a kan ‘yan uwansu larabawa a Yemen tsawon shekaru shida a jere, su ne suke zargin kasarsa da haifar da rikici a cikin kasashen larabawa.

Khatib Zade ya ce, zai fi ga kasashen da suke gudanar da irin wadannan taruka da su fuskanci gaskiya, su dawo su zauna tsakaninsu da dukkanin kasashen yankin, domin tattaunawa, da kuma samo hanyoyin warware matsalolin da ake fuskanta, maimakon yin tuhumce-tuhumce marasa kan gado a kan wasu kasashen.

3957745

 

 

captcha