IQNA

20:51 - March 08, 2021
Lambar Labari: 3485727
Tehran (IQNA) Kungiyar kasashen musulmi ta fitar da bayanin yin tir da Allawadai da harin da aka kai a wani dakin cin abinci a birnin Mugadishu na kasar Somalia.

Kamfani dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ya fitar, babban sakataren kungiyar kasashen musulmi Yusuf  Bin Ahmad Al-uthaimin ya bayyana cewa, harin da aka kai a birnin Mugadishu wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 20 da jikkatar 30 abin yin tir da Allawadai ne.

Ya ce babu wani dalili na kisan jama’a babu gaira babu sabar, kuma masu danganta hakan da addini ko jihadi, jahilan addini ne, masu aikata ta’addanci da sunan muslunci, wanda kuma musulmi suna nesanta kansu daga irin wadannan munanan ayyuka.

Bayanin ya ci gaba da cewa, kungiyar kasashen musulmi ba ta lamunta da ci gaban hakan ba, tare da yin kira da a kara kaimi wajen daukar matakan da suka dace domin tunkarar irin wadannan ayyuka na ta’addanci.

Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki nauyin kai harin, amma tuni aka zargi kungiyar al-shabab da hannu a wannan hari.

3958269

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: