IQNA

Rauhani: Ci Gaba Da Kakaba Takunkumi Kan Iran Da Amurka Take Yi Aiwatar Da Bukatar Yahudawa Ne

21:39 - March 10, 2021
Lambar Labari: 3485732
Tehran (IQNA) Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya bayyana cewa, ci gaba da kakaba takunkumin da Amurka take yi kan Iran aiwatar da manufofin yahudawa ne a kan kasar ta Iran.

A lokacin da yake gabatar da jawabi a yau a zaman bangaren zartarwa na kasar Iran, shugaban kasar Dr. Hassan Rauhani ya bayyana cewa, ci gaba da kakaba takunkumin da Amurka take yi kan Iran aiwatar da manufofin yahudawa ne, wanda kuma hakan ba mashala ce ga ita kanta Amurka ba.

Rauhani ya ce, abin da ya rage a gaban Amurka shi ne ta dawo ta bi dokoki da ka’idoji na kasa da kasa, kuma yin hakan abin jin kunya ba ne, matukar dai sabuwar gwamnatin kasar ta Amurka tana son ta dawo da mutuncin kasar da ya zube musamman a lokacin gwamnatin da ta gabata.

Ya ci gaba da cewa, dole ne Amurka ta janye dukkanin takunkumanta  a kan Iran, kafin duk wata tattaunawa a kan batun yarjejeniyar nukiliya, kuma babu batun sake wannan yarjejeniya, domin kuwa an riga an rattaba hannu a kanta, abin ya rage shi ne dukkanin bangarori da suka hada da ita kanta Amurka, su yi aiki da ita.

 

015

captcha