IQNA

11:10 - March 14, 2021
Lambar Labari: 3485741
Tehran (IQNA) Gwamnatin Jihar Neja a Najeriya ta bayar da umarnin rufe duka makarantun gwamnati da ke fadin jihar har na tsawon mako biyu.

An cimma wannan matsaya ne bayan wata tattaunawa tsakanin gwamnatin jihar da jami'an tsaron jihar.

Za’a rufe makarantun ne daga ranar Juma'a 12 ga watan Maris zuwa 26 ga watan na Maris.

An dau wannan matakin ne don bai wa jami'an tsaro lokaci da damar yin nazari kan duka makarantun gwamnati da ke jihar.

Hakan kuma zai bada damar duba hanyoyi daban daban da za’a inganta harkar tsaro da gine gine makarantun.

A kwanan baya ne dai ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mutane 42 na makarantar sakadaren Kagara, kafin daga bisani su sako su.

abna24

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: