IQNA

14:53 - March 15, 2021
Lambar Labari: 3485743
Tehran (IQNA) Firayi ministan haramtacciyar ƙasar Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewar ya soke ziyarar da ya so kai wa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ne ta hanyar sararin samaniyyar Saudiyya saboda tsoron makamai masu linzami na dakarun ƙasar Yemen.

A wata hira da yayi da tashar talabijin t a 13 ta Isra’ilan, Netanyahu ya ce ya soke ziyararsa ta farko zuwa UAE ɗin a makon da ya wuce ne saboda akwai matsaloli a sararin samaniyyar Saudiyya, yana mai ishara da hare-haren mayar da martani na baya-bayan nan da dakarun Yemen ɗin suka kai cikin Saudiyya.

A makon da ya wuce ɗin ne dai ƙasar Jordan ta hana jirgin Netanyahun bin ta sararin samaniyyar ƙasar saboda wani rikici da ya kunno kai tsakanin Jordan da Isra’ilan, don haka ya zama dole Netanyahun ya bi ta sararin samaniyyar Saudiyya don tafiya UAE ɗin lamarin da ka iya sanya jirgin nasa cikin hatsarin cin karo da makamai masu linzami na dakarun Yemen ɗin.

Wannan dai shi ne karo na huɗu da Netanyahun ya ke soke ziyarar da ya ke son kai wa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawan tun bayan da Isra’ila ta cimma yarjejeniyar hulɗar diplomasiyya da UAE ɗin

A da dai an shirya Netanyahun zai gana da firayi ministan UAE ɗin kuma yarima mai jiran gado na ƙasar Mohammed bin Zayed. Wasu rahotannin sun ce akwai yiyuwar Netanyahun ya gana da yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhammad bin Salman haka da kuma firayi ministan Sudan Abdalla Hamdok a yayin wancan ziyarar.

http://hausatv.com

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: