IQNA

Matashi Makaho Mai Karatun Digiri Na Uku A Fannin Shari’a A Maorocco

23:46 - March 16, 2021
Lambar Labari: 3485747
Tehran (IQNA) Abdulrahman Adzar matashi ne dan kasar Morocco da yake da burin ganin ya kamala hardar kur’ani baki daya

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Abdulrahman Adzar matashi ne dan kasar Morocco da yake da burin ganin ya kamala hardar kur’ani baki daya domin ya mayar da hakan ya zama bangaren da zai rika koyarwa.

Abdulrahman ya rasa ganinsa tun yana dan watanni biyu da haihuwa, saboda haka ya yi karatu a makarantar masu fama da larurar gani.

Bayan nan ya shiga jami'a, inda ya yi karatu a bangaren harshe da adabin Faransanci, daga nan kuma sai ya shiga bangaren digiri na biyu inda ya karanci ilimin shari'a kuma  a halin yanzu yana karatun a bangaren digiri na uku a wannan fage.

Sannan kuma a lokaci guda yana hardar kur'ani, inda yake da burin ganin bayan kammala hardar kur'ani da kuma digirinsa na uku, zai koma koyar da kur'ani mai tsarki.

 

3959738

 

 

captcha