IQNA

10:40 - March 18, 2021
Lambar Labari: 3485753
Tehran (IQNA) jakadan kasar Lebanon a Majalisar Dinkin Duniya ya mayar wa Isra’ila da martani kan zargin Hizbullah da ta’addanci.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, Salim Badura jakadan kasar Lebanon a Majalisar Dinkin Duniya, ya mayar da kakkausan martani kan kalaman jakadan Isra’ila, bisa zargin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da aikata ta’addanci.

Jakadan na Lebanon ya bayyana cewa, zargin kungiyar Hizbullah da aikata ta’addanci yana a matsayin cin zarafi ga dukkanin al’ummar Lebanon, domin kuwa kungiyar Hizbullah bangare ne mai matukar muhimmanci ta fuskar siyasa da wakiltar mutane masu yawa a kasar.

Ya ce Isra’ila ba ta hurumin da za ta zargi wani da ta’addanci, musamman ma idan batun ya shafi Lebanon, domin kuwa Isra’ila ce ta aikata ta’addanci a kan al’ummar Lebanon wand aba su manta da shi ba.

Jakadan na gwamnatin yahudawa a majalisar dinkin duniya ya yi suka kan kungiyar Hizbullah tare da bayyana cewa ita ce babbar barazana ga Isra’ila, kuma ita ce kungiyar ta’addanci a wurin Isra’ila.

 

3960371

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: majalisar dinkin duniya ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: