A bias rahoton kamfanin dillancin labaran iqna, a yammacin jiya ne ranar 1 ga watan Farvardin watan farko na shekarar hijira Shamsiyya ta 1400, jagoran juyin juya halin musulunci nan a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da jawabi ga al’ummar kasar.
Jawabin nasa dai ya mayar da hankali kan batutuwa daban-daban da suka shafi siyasar kasar, ta cikin gida da kuma ta waje, amma kafofin yada labarai sun fi mayar da hankali kan kalamansa da suka shafi matsayar kasar kan lamurra na kasa da kasa.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya tabo maganar jagora dangane da batun da ya yi cewa kasar Iran ba za ta dkatar da jingine yin aiki da wasu bangarorin yarjejeniyar nukiliya ba, har sai Amurka ta janye dukkanin takunkuman da ta dora wa Iran.
Tashar Alarabiyya ta Saudiyya kuwa, ta kawo bangaren maganarsa, dangane da irin makircin da makiya suke kitsawa Kasarda nufin ganin sun yi tasiri a cikin zabukan kasar masu zuwa.
Reuters ya kawo batun da ya yin a cewa, kasar ba ta gaggawa kan batun komawa ga yin aiki da yarjejeniyar da aka kulla kan batun nunkiya a shekara ta 2015.
Sputnik ya ambaci kalamin jagora dangane da wajabcin dauke dukkanin takunkumai a kan Iran, a matsayin sharadi guda daya tilo da ya zama wajibi Amurka ta yi aiki da shi, kafin cimma duk wata matsaya kan shirin Iran na nukiliya.
Tashar Russia Today kuwa ta ambaci cewa, jagoran ya jaddada cewa sabuwar gwamnatin Amurka ba za ta yi nasara ba wajen yin matsin lamba a kan Iran, kamar yadda gwamnatin da ta gabata ma ba ta yi ba.
Ita kuwa tashar Aljazeera ta kawo bangaren da yake cewa, Idan sabuwar gwamnatin Amurka ta zabi bin salon siyasar gwamnatin da ta gabace ta, to sai a ci gaba da tafiya a hakan.
Almayadeen ta kawo bangaren da yake cewa, a lokacin mulkin jam’iyyar Democrat ne Saudiyya ta fara kaddamar da yaki kan al’ummar Yemen, kamar yadda kuma ko a lokacin tana hada kai da Isra’ila wajen cutar da al’ummar musulmi a Falastinu.
Sai kuma tashar Almanar ta kawo batun zabe da kuma yadda jaggoran na juyin Iran ya jaddada wajabcin zaben shugaban kasa mai addini da kuma kishin al’ummarsa.