IQNA

17:03 - March 31, 2021
Lambar Labari: 3485774
Tehran (IQNA) wata cibiyar ayyukan alhairi ta kasar Turkiya ta raba kwafin kur’ani fiye da dubu 700 a wasu kasashen nahiyar Afirka.

Kamfanin dillancin labaran Turk Press ya bayar da rahoton cewa, Ali Usman Islahanchi mataimakin shugaban cibiyar ya bayyana cewa, suna gudanar da wadannan ayyuka ne a kasashen da aka fi bukata.

Ya ce duk da cewa har yanzu wasu yankuna suna yin amfani da alluna ne da ake sassakawa daga ita ce, amma duk da haka a irin wadannan wuraren ma ana kai kwafin kur’ani.

Ya kara da cewa, ya zuwa yanzu sun raba kwafin kur’ani guda dubu 722, da 999, da kuma kwafin littafin surat Yasin guda dubu 242 da 450.

Kasashen Nijar da Burkina Faso ne dai suka fi samun kaso mai yawa a cikin wadannan littafai a tsakanin kasashen yammacin nahiyar Afirka.

 

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3961701

Abubuwan Da Ya Shafa: alluna ، ayyuka ، sassakawa ، amfani ، mataimakin ، littafai
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: