IQNA

An Dakatar Da Gudanar Da Sallar Juma’a A Masallatai A Kasar Austria Saboda Corona

19:15 - April 03, 2021
Lambar Labari: 3485779
Tehran (IQNA) babbar cibiyar musulmi a kasar Austria ta sanar da rufe masallatan Juma’a a kasar sakamakon sake barkewar corona a kasar.

Kamfanin dillancin labaran KUNA ya bayar da rahoton cewa,  sakamakon sake barkewar corona a kasar Austria, babbar cibiyar muuslmi a kasar ta sanar da rufe masallatan Juma’a a kasar, da kuma takaita dukkanin taruka na addini da suke hada jama’a.

A cikin lokutan baya-bayan nan mahukunta a bnagren kiwon lafiya a kasar Austria sun sanar da cewa an shiga zango na hudu na sabuwar cutar corona, wanda yake da matukar hadari.

Bayanin ya ce an hana gudanar da taruka da suke hada cunkoson jama’a a wiri guda, tare da wajabta sanya takunkumin rufe baki da hanci da zaran mutum ya fito daga gida, wanda hakan yasa musulmi suka dauki matakan dakatar da tarukan sallar Juma’a a kasar baki daya.

Akwai musulmi fiye da dubu 800 a kasar Austria, wanda hakan ke nufin cewa su ne na biyu a kasar bayan kiristocin darikar Katolika.

 

3962205

 

 

 

captcha