IQNA

An Soki Shugaba Al Aisi Kan Girmama Sarakunan Fira’aunoni Na Masar

12:14 - April 06, 2021
Lambar Labari: 3485789
Tehran an soki lamirin shugaban kasar Masar kan kirkiro ranar girmama sarakunan Fira’aunoni da aka yi a kasar ta Masar.

Tashar TRT ta bayar da rahoton cewa, a cikin tsauraran matakan tsaro ne shugaban kasar Masar abdulfattah Al sisi ya halrci taron girmama sarakunan Fira’aunoni a birnin Alkahira.

A ranar ta jiya an fito da akwatunan gawawwaki na sarakunan da aka yia  kasar Masar dubban shekaru  da suka gabata, domin dauke su daga wuraren da suke zuwa wani dakin ajiyar kayan tarihi sabo da aka gina.

Babbar manufar hakan ita ce kirkiro wata rana ta musamman domin tunawa da sarakunan da suka yi mulki da ake yi sarautarsu taken fir’ana dubban shekaru da suka gabata a kasar Masar.

To sai dai wasu daga cikin masana kan harkoki na addini na ganin hakan ya sabawa shari’a, domin kuwa littafan da aka saukar daga sama da suka yi bayani kan sarautar fir’auna, suna bayyana shi a matsayin mutum azzalumi.

Umar Ali, masani kan harkokin tarihi da kuma addinai, ya bayyana cewa; abin da Al sisi ya yi ya saba wa abin da yake a cikin addinin kirista da musulunci, domin kur’ani da Linjila duk sun ambaci Fir’auna a matsayin sarki masharranci, saboda haka girmama shi yana karo da abin da ke cikin wadannan littafai.

Tun lokacin tsohon shygaban kasar Masar Husni Mubarak ne ya nemi kirkiro wata rana makamanciyar haka, amma sakamakon sukar hakan da al’ummar Masar suka yi, ala tilas Husni Mubarak ya janye shirin nasa.

 

3962698

 

captcha