IQNA

22:00 - April 10, 2021
Lambar Labari: 3485796
Tehran (IQNA) Firayi ministan kasar Singapore ya bayyana cewa musulmi mata masu aikin jinya a asibitoci za su iya saka lullubi a kansu.

Shafin yada labarai an Channels News ya bayar da rahoton cewa, Lee Hsein Loong Firayi ministan kasar Singapore ya bayyana cewa musulmi mata masu aikin jinya a asibitoci za su iya saka lullubi a kansu a lokutan aiki.

Ya ce wannan lamari da suka jima suna tattaunawa  akansa, kuma yanzu ya bayar da umani ga gwamnati domin ta tsara yadda lamarin zai kasance, ta yadda mutane za su samu masaniya kan hakan a kasa baki daya.

Ya ci gaba da cewa, kasar Singapore kasa wadda ta hada al’ummomi da addinai daban-daban, akan haka yana da kyau kowane bangare a kiyaye masa hakkinsa na addini daidai da koyarwar addininsa.

Masagos Zulkifli, minister mai kula da harkokin da suak shafi musulmi a kasar Singapore ya bayyana cewa, wannan lamari ne mai matukar muhimmanci da ya kamata ya zama abin koyi domin kawo karshen nuna wariya ta addini.

3963493

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: