IQNA

Daruruwan Falastinawa Sun Shiga Aikin Gayya Na Share Masallacin Quds Mai Alfarma

23:48 - April 11, 2021
Lambar Labari: 3485799
Tehran (IQNA) daruruwan Falastinawa sun shiga cikin aikin gayya na shekara-shekara da ake yi na share masallacin Quds kafin watan Ramadan.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, a yau daruruwan Falastinawa sun shiga cikin aikin gayya da ake yi na share masallacin Quds kafin watan Ramadan mai alfarma a kowace shekara, tare da halartar Falastinawa daga dukkanin sassa.

A wannan shekaar ana gudanar da wanann aikin ne tare da daukar matakai na kiwon lafiya sakamakon matsalar da ake famaa da ita ta yaduwar cutar korona a duniya.

Daga cikin ayyukan da ake gudanarwa dai har da share masallacin quds baki dayansa, da hakan ya hada da wanke dukkanin sassan masallacin ciki da waje, da kuma kakkabe dardumunsa da share kura daga kan abubuwan da suke cikin masallacin.

Baya ga haka kuma ana gudanar da shirye-shirye na addini a cikin watan ramadan a wannan masallaci mai alfarma kuma alkiblar musulmi ta farko, wanda a halin yanzu yake karkashin mamayar yahudawan Isra'ila.

 

3963569

 

captcha