IQNA

Yanayin Watan Ramadan Mai Alfarma A Kasashen Duniya

19:51 - April 12, 2021
Lambar Labari: 3485801
Tehran (IQNA) a gobe ne za a fara azumin watan ramadan a wasu daga cikin kasashen duniya.

Shafin jaridar Al-dastur ya bayar da rahoton cewa, a  daidai lokacin da watan ramadan yake karatowa musulmia  ko’ina cikin fadin duniya suna yin shiri na tarbar wannan wata mai albarka.

A kowace shekara musulmi suna azumtar watan ramadana  matsayin daya daga cikin ayyukan ibada na farilla da Allah ya wajbta musu, saboda haka dukkanin musulmi suna girmama wannan lokaci na wannan ibada mai girma.

A gobe ne dai wasu daga cikin kasashen msuulmi za su tashi da azumi, bayan da suka sanar da cewa jiya Lahadi ba a ga watan ramadan ba, inda aka cika kwanaki talatin a yau Litinin.

A wanann shekarar ma kamar shekarar da ta gabata ana fuskantar matsalar yaduwar cutar korona, said ai wanann shekarar akwai sauki idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, inda aka shiga kulle a dukkanin kasashe a lokacin watan ramadan.

Yanayin Watan Ramadan Mai Alfarma A Kasashen Duniya

Wasu daga cikin kasashen musulmi sun bayyana yanayin nab ana da cewa za a iya samun damar gudanar da wasu daga cikin ayyukan da aka saba yi kamar sallar asham, yayin da kuma wasu kasashen suka ce za a takaita lokacin sallar.

 

3963746

 

 

 

 

captcha