IQNA

An Bude Baje Kolin Kur'ani A Masallacin Haramin Makka Mai Alfarma

23:32 - April 27, 2021
Lambar Labari: 3485852
Tehran (IQNA) shugaban hukumar da ke kula da masallacin harami da masallacin manzon allah (SAW) ya sanar da bude baje kolin kur'ani a masallacin haramin Makka mai alfarma.

Shafin yada labarai na jaridar Alyaum ya bayar da rahoton cewa, Abdulrahman Al-sudais, shugaban hukumar da ke kula da masallacin harami da masallacin manzon allah (SAW) ya sanar da bude baje kolin kur'ani a masallacin haramin Makka mai alfarma.

Ya ce babbar manufar wannan baje koli ita kara yada lamarin kur'ani da kuma yin amfani da wannan dama ta lokacin Ramadan.

Ya ce ana gudanar da baje koli ne tun daga karfe 12 na rana har zuwa karfe 2 na dare, wurin yana bude ga dukkanin wadanda suke son zuwa domin duba abubuwa da aka saka  da suka shafi kur'ani.

Baya ga haka kuma ya bayyana cewa, akwai shafuka na yanar gizo wadanda aka bude wadanda suka shafi wanann baje koli, wanda za aiya ziyartarsu domin dubawa.

 

 

3967220

 

 

captcha