IQNA

Qatar Ta Yi Allawadai Da Farmakin Yahudawan Isra’ila A Kan Masallacin Quds

14:55 - April 29, 2021
Lambar Labari: 3485858
Tehran (IQNA) kasar Qatar ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da farmakin da yahudawan Isar’aila suka kaddamar a kan masallacin Quds.
 

A rahoton da kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar, ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar ta fitar da wani bayani a yammacin jiya, wanda a cikinsa ta sanar da cewa, gwamnatin kasar tana yin tir da Allawadai da kakkausar murya dangane da farmakin da yahudawan Isar’aila suka kaddamar a kan masallacin Quds tare da jikkata musulmi masallata a cikinsa.

 Bayanin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Qatar ya ce, daukar irin wannan mataki da Isra’ila take yi a kan musulmin Falastinu da kuma keta alfarmar masallacin Quds, abu ne wanda yake sosa ran kowane musulmi a duniya, kuma hakan ci gaba ne na ayyukan mamayar Isra’ila a kan yankunan Falastinawa.

 Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, take hakkokin Falastinawa da zaluntarsu da Isra’ila ke yi, yana a matsayin take hakkokin bil adama ne, wanda ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na duniya.

 Ko a jiya Jami’an tsaron yahudawan Isra’ila sun kai farmaki kan musulmi a masallancin Quds a lokacin sallar Asham, inda suka lakada musu duka, wanda hakan ya yi sanadiyyar jikkatar da dama daga cikinsu, inda yanzu haka fiye da mutane 100 daga cikinsu suna kwance a asibiti.

 

3967875

 

captcha