IQNA

An Fara Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Kan Masallacin Quds

21:48 - May 05, 2021
1
Lambar Labari: 3485880
Tehran (IQNA) an fara gudanar da taro na kasa da kasa kan masallacin da Iran take daukar nauyinsa.

Wannan taro a kan masallacin Quds ta hanyar bidiyo daga nesa, shi ne irinsa na biyu, saboda bullar cutar corona, kuma baki ne daga cikin gida da waje za su yi bayanai domin raya ranar Kudus ta duniya.

Bakin za su yi jawabai ne a cikin harsunan Farsi, turancin Ingilishi, da kuma Larabci, wanda za a watsa kai tsaye.

Daga cikin jigo-jigo da za a tattauna da akwai batun kare hakkin dan’adam,mamayar da ‘yan sahayoniya su ka yi wa birnin Kudus mai tsarki da kuma kudurorin da majalisar dinkin duniya ta fitar akan wannan birnin.

Masu gabatar da jawabai sun kai 30 daga kasashen Iran, Palasdinu, Malaysia, India, Pakistan, Fransa, Argentina, Iraqi. Sai kuma Turkiya, hadaddiyar daular larabawa, Lebanon, Syria, Burtaniya, Canada da Tunisiya.

Musulmi a ko’ina a duniya suna raya juma’ar karshe ta kowance azumin watan Ramadan a matsayin ranar Kudus, bisa umarnin marigayi Imam Khomaini tun bayan cin nasarar juyin juya halin musulunci a Iran.

 

3969482

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
mukhtar usman
0
0
ALLAH YABADA SA.A AMMA BABU MUTUM KODAYA A NIGERIA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :