IQNA

Duniya Na Ci Gaba Da Yin Allawadai Da Ta'asar Isra'ila A Birnin Quds

23:38 - May 10, 2021
Lambar Labari: 3485899
Tehran (IQNA) duniya suna ci gaba da yin Allawadai da ta’asar da gwamnatin yahudawan sahyuniyya take tafkawa a birnin Quds.

Bangarori daban-daban na duniya suna ci gaba da yin Allawadai da ta’asar da gwamnatin yahudawan sahyuniyya take tafkawa a birnin Quds.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, bangarori daban-daban a duniya suna ci gaba da yin kira ga Isra’ila da ta dakatar da abin da take yi na kai farmaki kan wurare masu tsarki na musulmi a cikin birnin Quds.

Babban jagoran mabiya addinin kirista na darikar Katolika Paparoma Francis, ya bayyana matukar damuwarsa dangane da abin da yake faruwa a Quds, inda ya yi kira da a gaggauta kawo karshen yamutsi da ke alfarmar wurare masu tsarki.

A nasu bangaren gwamnatocin kasashen musulmi da na larabawa da dama sun yi tir da abin da Isra’ila take aikatawa kan musulmi a birnin Quds, musamman a kan masallaci mai alfarma, inda take keta alfarmar wannan masallaci ta hanyar kai hari a kan masallata a cikinsa.

Gwamnatocin kasashen Iran, da kuma Iraki, gami da Turkiya da Jordan da kuma Lebanon, Aljeriya da Tunisia da sauransu, sun yi kakkauasar suka kan gwamnatin yahudawan Isra’ila dangane da ta’asar da take tafkawa a kan musulmin birnin Quds, tare da kiran bangarori na kasa da kasa da a dauki mataki na bai daya domin taka mata burki.

Kungiyar kasashen larabawa ta kirayi zaman gaggawa wanda za a gudanar a gobe Talata, wanda zai samu halartar ministocin harkokin wajen kasashe mambobi na kungiyar, domin tataunawa kana bin da yake faruwa a Quds, da kuma matakin da za su dauka kan hakan.

 

 

3970452

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :