IQNA

Falastinawa 24 Ne Suka Yi Shahda A Gaza Sakamakon Hare-Haren Yahudawan Isra'ila

23:53 - May 11, 2021
Lambar Labari: 3485906
Tehran (IQNA) Akalla Falastinawa 24 ne suka yi shahada daga daren jiya Litinin zuwa safiyar yau Talata, a hare-haren da jiragen yakin Isra’ila suka kaddamar a kan Falastinawa.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, daga daren jiya Litinin zuwa safiyar yau Talata, sakamakon hare-haren da jiragen yakin Isra’ila suka kaddamar a kan Falastinawa da ke yankin zirin Gaza, Akalla Falastinawa 24 ne suka yi shahada, da suka hada da yara 9 da kuma mace daya.

Rahoton ya ci gaba da cewa, sojojin yahudawan Isra’ila sun kaddamar da hare-hare a kan yankuna daban-daban na yankin zirin Gaza a yammacin jiya, inda hare-haren suka nufi gidajen jama’a da tituna da mutane suke taruwa, wanda hakan ne ya yi sanadiyyar yin shahadar mutane akalla 24, da kuma jikkatar wasu 103.

Sai dai a nasu bangaren kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa sun mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami a kan matsugunnan yahudawa da kuma wasu birane, da hakan ya hada har da birnin Tel Aviv.

A birnin Quds kuwa a daren jiya jami’an tsaron yahudawan sun ci gaba da kaddamar da farmaki a kan masallata, tare da harba harsasai da hayaki mai sanya hawaye a cikin masallacin Aqsa, inda suka jikkata masallata fiye da 600, kamar dai yadda kungiyar bayar da agajin gaggawa ta falastinu ta tabbatar.

 

captcha