IQNA

Likitocin Masar 1200  Sun Sanar Da Shirinsu Na Zuwa Gaza Domin Taimaka Ma Wadanda Isra'ila Ta Jikkata

22:52 - May 16, 2021
Lambar Labari: 3485921
Tehran (IQNA) yanzu haka akwai likitoci 1200 da suka yi rijistar sunayensu domin zuwa Gaza da nufin taimaka wa wadanda Isra’ila ta jikkata

Kungiyar likitoci a kasar Masar ta sanar da cewa, yanzu haka akwai likitoci 1200 da suka yi rijistar sunayensu domin zuwa Gaza da nufin taimaka wa wadanda Isra’ila ta jikkata.

Tashar Russia Today tabayar da rahoton cewa, Usama Abdulhayyi babban sakataren kungiyar likitoci ta kasar Masar ya bayyana cewa, ya zuwa yau Lahadi likitoci 1200 da suka yi rijistar sunayensu domin zuwa Gaza da nufin taimaka wa wadanda Isra’ila ta jikkata a hare-haren da take kaddamarwa a kan al’ummar yankin.

Ya ci gaba da cewa, likitocin suna bayar da gudunmawa ga Falastinawan da aka shigo da su cikin kasar ta mashigar Rafah wadda ta hada yankin arewacin masar da zirin Gaza, inda yanzu haka an shigar da Falastinawa da suka samu munanan raunkua a cikin kwanaki bakawai da yahudawan Isra’ila suak kwashe suna lugen wuta kan al’ummar yankin na zirin Gaza.

Babban sakataren kungiyar likitoci ta kasar Masar ya ci gaba da cewa, likitocin da suka yi rijistar sunayensu nasu suna jiran gwamnatin Masar ta ba su izinin shiga cikin yankin zirin Gaza, inda suka shirya kayan aiki da motocin daukar marasa lafiya da kuma wasu daga cikin kayayaklin aikin gaggawa domin ceto rayukan wadanda suka samu munanan raunuka.

 

3971832

 

 

 

captcha