A wata zantawarsa da tashar France 24, shugaban kasar Afirka ta kudu Cyrill Ramaphosa ya bayyana cewa, abin da yake faruwa a kan al’ummar Gaza yana tuna masa da mulkin wariya a Afirka ta kudu a shekarun da suka gabata.
Ya ce gwamnatin Afirka ta kudu tana goyon bayan al’ummar Falastinu, amma duk da haka yana kira ga bangarorin biyu da su zauna kan teburin tattaunawa kamar yadda aka yi a kasar Afirka ta kudu a shekara ta 1990.
Ramaphosa ya ce; munanan hare-haren sojojin Isra’la a kan fararen hula a yankin Gaza, tare da kashe mata da kananan yara da kuma fitar da mutae daga gidajensu suna gudu domin tsira da rayukansu, yana kara tabbatar da cewa har yanzu akwai sauran mulkin wariya a duniya.
A cikin wani bayani da ya saka a shafinsa na twitter a jiya Talata, shugaban kasar Afirka ta kudu Cyrill Ramaphosa ya bayyana cewa, irin abin da yake faruwa kan al’ummar Gaza, yana tuan musu da abin da ya faru a Afirka ta kudu a tsakanin shekarun 1948 zuwa 1994, inda ya ce sau biyu danginsa ‘yan uwansa da iyayensa suna sauya yankunan da suke rayuwa saboda gallazawar da aka yi musu.