Shafin yada labarai na jariar al-ahad ya bayar da rahoton cewa, Abdullatif Alqanu mai magana da yawun kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ya gargadi jami’an tsaron Isra’ila, dangane da ci gaba da tsokanar Falastinawa da suke yi a birnin Quds da unguwar Sheikh Jarrah da ke gabashin.
Abdullatif Alqanu ya ce; ‘yan sa’oi bayan fara aiki da yarjejeniyar dakatar da bude wuta a daren Juma’a, a ranar Juma’a jim kadan bayan kammala sallar Juma’a a masallacin Quds, jami’an tsaron Isra’ila sun auka wa musulmi a lokacin da suke fitowa daga masallaci.
Ya ce jami’an tsaron yahudawan sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa masallatan, tare da lakada wa wasu daga cikinsu duka da kulake.
Mai magana da yawun kungiyar ta Hamas ya ce, idan wannan yanayin ya ci gaba a haka, duk abin da ya biyo baya Isra’ila ce ke da alhakin hakan, domin kuwa yana a matsayin karya yarjejeniyar da aka yi, inda daya daga cikin sharuddan Hamas kafin amincewa da dakatar da bude shi ne Isra’ila ta daina keta alfarmar masallacin Quds ko cin zarafin masallata a cikinsa, wanda Isra’ila ta amince da hakan.