IQNA

Macron Ya Yi Barazanar Janye Sojojin Faransa Daga Mali Idan Kasar Ta Karkata Ga Tsatsauran Ra’ayin Addini

23:04 - May 30, 2021
Lambar Labari: 3485966
Tehran (IQNA) Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya yi barazanar janye dakarun kasarsa daga Mali idan ta kama hanyar zama kasa mai tsatsaurin ra’ayin Islama.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Macron ya bayyana hakan a wata tattaunawa da jaridar Journal du Dimanche JDD, ya kuma jadadda goyan bayansa ga tattabatar da mulkin rikon kwarya, bayan abunda ya danganta da juyin mulki da ba za’a lamunta da shi ba.

Faransa dai ta girke kusan dakaru 5,000 dake aiki a karkashin rundunar Barkhane wacce ke dafawa Mali a yakin da take yi da yan ta’ada tun a shekara ta 2012.

Kallaman na Macron na zuwa ne gabanin taron da shugabanin kasashen yammacin Afrika ke gudanarwa a kasar Ghana yau Lahadi, kan halin da ake ciki a Mali, game da juyin mulkin da sojoji sukayi a makon jiya, wanda shi ne karo na biyu a cikin watanni tara.

Kungiyar ECOWAS, ta sanya takunkumi kan Mali bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Agustan da ya gabata, amma an dage bayan yarjejeniyar dawo da mulki ga farar hula.

Yanzu jagoran juyin mulkin, Kanal Issimi Goita, shi ne kotun tsarin mulkin kasar ta ayyana a matsayin shugaban kasar ta Mali.

 

3974608

 

captcha