IQNA

Taruka 273 Domin Tunawa Da Marigayi Imam Khomeini A Kasashen Duniya Daban-Daban

22:31 - June 02, 2021
Lambar Labari: 3485974
Tehran (IQNA) Ana shirin gudanar da taruka na tunawa da marigayi Imam Khomeini a karkashin ofisoshin jakadancin Iran da ke kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da cibiyar yada al’adun muslunci ta kasar Iran ta fitar, ta sanar da cewa shugaban cibiyar Abuzar Ibrahimi Turkman ya bayyana cewa, a wannan shekara za a gudanar da taruka da shirye-shirye a kasashen duniya daban-daban, dangane da zagayowar lokacin tunawa da rasuwar marigayi Imam Khomeini, wanda ya kafa Jamhuriyar Muslunci ta Iran.

Ya ce akwai taruka da dama wadanda wasu cibiyoyi masu zaman kansu za su gudanar a wasu kasashe, da suka hada da cibiyoyin addini da kuma na ilimi, gami da kungiyoyin fafutuka da dai sauransu, wanda hakan taruka ne na cibiyoyi da kungiyoyi masu zaman kansu a kasashen duniya daban-daban.

Dangane da tarukan da  cibiyar yada al’adun muslunci ta kasar Iran za ta dauki nauyin shiryawa a kasashe duniya duniya kuwa, za su gudana a nea  karkashin kulawar ofisoshin jakadanci na Iran da suke a kasashe fiye da 80 na duniya.

Ya ce wasu tarukan za su gudana ne ta hanyar taro na jama’a a manyan dakunan taro, tare da kiyaye ka’idoji na kiwon lafiya, yayin da kuma wasu tarukan za su gudana ne ta hanyar yanar gizo, inda masana da ‘yan siyasa da malamai za su gabatar da jawabai a kan maudu’ai daban-daban da suka shafi rayuwar marigayin, da kuma irin darussan da za a iya dauka daga rayuwarsa ta ilimi da gwagwarmayar neman tabbatar da adalci a duniya.

3975314

 

captcha