IQNA

Mahukuntan Saudiyya Sun Sare Kan Wani Yaro Da Takobi Bisa Zarginsa Da Yi Musu Tawaye

22:45 - June 16, 2021
Lambar Labari: 3486019
Tehran (IQNA) gwamnatin Saudiyya ta kashe wani matashi bisa zarginsa da yi wa sarki bore.

Кungiyoyin kare haƙƙoƙin bil’adama na ƙasa da ƙasasun yi tir da ƙasar Saudiyya saboda zartar da hukuncin kisa kan wani saurayi bisa zargin bore wa gwamnati  a lokacin yana ɗan ƙaramin yaro.

A jiya Talata ne dai gwamnatin Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa a kan Mustafa bin Hashem bin Issa al Darwish, saurayin da ya fito daga yankin Qatif , inda suka zargi Mustafa ɗin ne da laifin ɗaukar makami don yaƙar masarautar, barazana ga tsaron ƙasa, ƙirƙirar ƙungiyar ta’addanci da nufin kashe jami’an tsaro da kuma tunzurawa don yin bore, bisa hakan ne wata kotu a Saudiyya ta yanke masa hukuncin kisar da aka zartar a jiyan.

Кungiyoyin kare haƙƙoƙin bil’adaman dai sun ce ba a yi wa matashin adalci ba yayin shari’ar bisa la’akari da cewa an tilasta masa ne amincewa da zargin da ake masa sannan kuma lokacin da aka kama shi bisa wannan laifin yana ƙasa da shekaru 17 ne, kamar yadda kuma suka yi zargin cewa tsawon lokacin da ake tsare da shi jami’an tsaron Saudiyyan sun ɗanɗana masa nau’oi daban-daban na azaba.

Iyayen matashin dai sun ce ba a sanar da su za a zartar da wannan hukuncin ba, su ma ta kafafen watsa labarai suka sami labari.

 

 

3977772

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: makami ، jami’an tsaro ، lokaci ، amincewa ، tilasta masa ، tunzurawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :