IQNA

22:32 - June 19, 2021
Lambar Labari: 3486026
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran ya jinjina wa al’ummar Iran saboda gagarumar fitowar da suka yi yayin zaɓen shugaban ƙasar.

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jinjina wa al’ummar Iran saboda gagarumar fitowar da suka yi yayin zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar jiya Juma’a yana mai bayyana al’ummar Iran ɗin a matsayin waɗanda suka yi nasarar.

Jagoran ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya fitar a yau Asabar

A cikin sakon ya gode wa al’ummar Iran ɗin saboda yadda suka fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu don zaɓan sabon shugaban ƙasa da kuma ‘yan majalisu daban-daban na ƙasar inda ya bayyana hakan a matsayin wani sabon shafi mai haskaka rayuwarsu.

Imam Khamenei ya ce irin fitowar da al’ummar suka yi abin jinjinawa ne duk kuwa da irin matsalolin da ake fuskanta da kuma bakar farfagandar da makiya suka dinga yi da nufin haka su fitowa.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Haƙiƙanin waɗanda suka yi nasara a yayin wannan zaɓen su ne al’ummar Iran waɗanda suka tsaya ƙyam da yin watsi da farfagandar maƙiya da ‘yan amshin shatansu wajen hana su fitowa.

Daga ƙarshe Jagoran ya gode wa cibiyoyin da suka shirya da kuma gudanar da zaɓen da kuma jami’an tsaro da suka tabbatar da tsaro bugu da ƙari hukumar gidan radiyo da talabijin ta ƙasa sakamakon irin gagarumin ƙoƙarin da ta yi wajen wayar da kan al’umma da kuma sanar da jama’a abin da ke gudana.

A jiya Juma’a ne dai aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasar karo na 13 na Iran inda sakamakon zaɓen ke nuni da cewa Sayyid Ibrahim Ra’isi shi ne ya lashe zaɓen da kasha 62% na kuri’un da aka kaɗa bayan ƙirga sama da kasha 90 cikin ɗari na kuri’un da aka kaɗa ɗin.

 

 

 

3978627

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: asabar ، jagoran juyin juya halin musulunci ، jinjina ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: