IQNA

Masani Daga Malaysia: Dr. Shari'ati Mutum Ne Da Ya Kara Fito Kimar Musulunci A Zamanance

22:37 - June 19, 2021
Lambar Labari: 3486027
Tehran (IQNA) Ahmad Farouq Musa masani ne dan kasar Malysia, wandaya bayyana Dr. Shari'ati a matsayin mutumin da ya kara fito da kimar musulunci a zamanance.

a wata tattaunawa da ya yi da kamfanin dillancin labaran iqna, Dr. Ahmad Farouq Musa masani dan kasar Malysia,  ya bayyana Dr. Shari'ati a matsayin mutumin da ya kara fito da kimar musulunci a zamanance ta hanyoyin bayanansa da kuma rubutunsa.

Dr. Ahmad Farouq Musa ya ce, Dr. Ali Shari'ati wanda masani ne dan kasar Iran wanda kimanin shekaru 44 rasuwarsa, ya kasance mutum ne mai kaifin basira da kwakwalwa ta mudsamman, wanda yake fahimtar lamurra ta fuskoki daban-daban, tare da bayyana su daidai da yadda za su amfanar da al'ummomi.

Daga cikin abubuwan da Dr. Shari'ati ya kebanta da su, har da yadda ya kasance kowane mutum daga kowane addini zai iya karanta littafansa ya amfana da su.

Ya yi amfani da hikima da zurfin iliminsa wajen bayyana addinin mulsunci ga al'ummomin da ba muuslmi ba a zamanance, wanda ya yi tasiri matuka musamman ma ga masana daga cikin irin wadanann mutane, ta wasunsu sun musulunta ta hanyar karatun littafansa.

Dr. Ali Shari'ati ya kasance yana adawa da salon mulkin kama karya na sarki Shah a Iran, kuma an kashe shi ne a birnin Landan na kasar Burtaniya a lokacin mulkin sarki Shah, wanda hakan yasa ake zargin cewa hadin baki ne tsakanin sarki Shah da gwamnatin Burtaniya.

3978068

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :