IQNA

YaddaKafofin Yada Labaran Waje Suka Watsa Rahotanni Kan Zaben Iran

22:59 - June 19, 2021
Lambar Labari: 3486028
Tehran (IQNA) Kafofin yada labarai da daman a duniya sun bayar da rahotanni dagane da zaben da aka gudanar a kasar Iran.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, tun jijjifin safiyar jiya Juma’a mutane suka fara yin dafifi a rumfunan zabe kafin bude rumfuna fiye da dubu 66 da aka ware domin kada kuri’u a fadin kasar ta Iran.

Rahoton ya ce tun da safiyar jiya ne jagoran juyin juya halin muslunci na kasar ta Iran ya fara kada kuri’arsa a daidai lokacin da aka fara kada kuri’a a hukumance, daga lokacin ne kuma aka ci gaba da kada kuri’a a fadin kasar.

Ita ma a nata bangaren tashar Russia Today ta bayar da rahotanni daga sassa daban-daban na kasar ta Iran dangane da yadda zaben ya gudana, tare da jin ra’ayoyin mutane daban-daban kan zaben.

Wasu daga cikin kafofin yada labaran sun bayyana cewa, daga ra’ayoyin masu kada kuri’a da suka ji, suka fahimci cewa Ibrahim Ra’isi dan shekaru 60 da haihuwa wanda yake rike da kujerar alkalin alakalan kasar, shi ne ya fi sauran ‘yan takarar damar lashe zaben.

Sky News ta bayar da rahoton cewa, zaben na Iran shi ne zaben shugaban kasa karo na goma sha uku da ake gudanarwa a kasar, wanda yake gudana bisa tsarin dimukradiyya da take tafiya bisa tsarin muslunci daidai da dokar kundin tsarin mulkin kasar

Tashar Almayadeen ta bayar da rahotanni daga birane daban-daban na kasar Iran, tare da hotuna kai tsaye a lokacin da ake gudanar da zabukan.

YaddaKafofin Yada Labaran Waje Suka Watsa Rahotanni Kan Zaben Iran

YaddaKafofin Yada Labaran Waje Suka Watsa Rahotanni Kan Zaben Iran

YaddaKafofin Yada Labaran Waje Suka Watsa Rahotanni Kan Zaben Iran

YaddaKafofin Yada Labaran Waje Suka Watsa Rahotanni Kan Zaben Iran

3978401

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :