IQNA

Jerin Gwano A Birnin Abuja Domin Yin Kira Da A Saki Sheikh Ibrahim Zakzaky

23:49 - June 22, 2021
Lambar Labari: 3486040
Tehran (IQNA) an gudanar da jerin gwano a birnin Abuja na Najeriya domin yin kira da a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Magoya bayan Harka Islamiyya sun gudanar da jerin gwano a birnin Abuja na Najeriya domin yin kira da a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran Harka Islamiyya a Najeriya da ake tsare da shi, tare da mai dakinsa Malama Zinat Ibrahim.

Wannan jerin gwano yana da cikin irinsa wanda magoya bayan Harka Islamiyya suke gudanarwa lokaci zuwa lokacia  cikin Abuja da ma wasu birane na Najeriya, domin yin kira da a saki Sheikh Zakzaky wanda ake tsare da shi tare da mai dakin nasa ba tare da wani hukunci ba.

Tun a karshen shekara ta 2015 ne dai jami'an sojin Najeriya suka kaddamar da farmaki kan cibiyar Husainiyar Baqiyatollah a Zaria, daga nan kuma suka fadada farmakin nasu har zuwa kan gidan Sheikh Zakzaky, bayan da suka bayyana cewa magoya bayan Harka Islamiyya sun tare wa babban hafsan sojin kasa na Najeriya Janar Tukur Burutai hanya.

A kan hakan sojojin suka kashe mutane masu yawa daga cikin magoya bayan Harka Islamiyya, tare da kama Sheikh Zakzaky da maidakinsa, wanda kuma tun daga lokacin ne ake tsare da su, ba tare da wani hukunci ba, inda kungiyoyin kare hakkin bil adama ke yin kira da a saki Sheikh Zakzaky da maidakinsa domin kula da lafiyarsu.

 

3979186

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: sheikh Ibrahim Zakzaky ، birnin Abuja ، Najeriya ، malama Zinat
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :