IQNA

‘Yan Sanda A Birnin New York Na Amurka Na Neman Wani Mutum Mai Cin Zarafin Mata Musulmi

22:18 - July 03, 2021
Lambar Labari: 3486072
Tehran (IQNA) jami’an ‘yan sanda a birnin New York na kasar Amurka sun sanar da cewa, suna neman wani mutum wanda yake cutar da mata musulmi masu sanye da hijabin musulunci.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, jami’an ‘yan sanda a birnin New York na kasar Amurka sun sanar da cewa, suna neman wani mutum wanda yake cutar da mata musulmi masu sanye da hijabin musulunci a cikin birnin.

‘Yan sandan sun bayyana cewa, mutum ya kai farmaki kan gungun mata musulmi masu sanye da lullubi a yankin Queens da ke cikin birnin na New York, a lokacin da ya kai musu harin kuma yana yi kalamai na cin zarafi ga manzon Allah (SAW) sannan ya tsere ba tare da an iya cimmasa ba.

Baya ga haka kuma wani mutum wanda ake zaton cewa dais hi ne, tare da taimakon wani da suke tare, sun kai wa wata mata musulma hari da take sanye da lullubi, wadda shekarunta za su kai 24, inda suka dake ta a fuska da kuma harbinta da kafa, kamar yadda kuma suka daki wani wani dan uwanta da yake tare da ita, wanda suka ji masa raunuka.

Jami’an ‘yan sandan New York sun nuna wani faifan bidiyo da kamara ta dauka na wani mutum da ake zaton cdwa shi ne yake aikata wannan ta’asa, sun kuma bukaci jama’a da su taimaka wajen gano shi domin kame shi.

3981525

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: taimaka ، farmaki ، mata musulmi ، wajen gano ، dan uwanta ، musulma
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha