IQNA

Kare Sahihiyar Kira'a Ta Kur'ani Da Hana Yaduwar Gurbatacciyar Kira'a

21:30 - July 05, 2021
Lambar Labari: 3486077
Tehran (IQNA) an fara daukar matakai na kare sahihiyar kira'a ta kur'ani mai tsarki a kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, hukumomin da ke kula da lamurran addini a kasar Masar sun kudiri aniyar tabbatar da cewa an hana yada duk wata kira'ar kur'ani da ba a san da ita ba a cikin kira'oin da aka sani tabbatattu.

Kwamitin kula da lamurran kur'ani a karkashin ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar ya sanar da cewa, an fara daukar kwararan matakai na tantance masu karatu da kuma nau'oin kira'a da suke amfani da su,

Bayanin ya ce daukar wannan mataki ya zama wajibi domin hana gurbata kir'ar kur'ani mai tsarki a cikin al'ummar musulmi.

Wannan na zuwa ne bayan da aka fara samun wasu sabbin masu karatu da suke kirkiro salon karatun kur'ani irin nasu a kasar Masar, lamarin da yake fuskantar kakakusar suka daga jama'a, tare da yin kira da a dauki mataki na kawo karshen hakan, domin tsare martabar kira'ar kur'ani mai tsarki.

Kasar masar ce dai tafi shahara a tsakanin kasashen musulmi wajen yawan makaranta kur'ani da suka yi suna a duniya tun tsawon shekaru, inda kuma har yanzu ana samun sabbin makaranta da suke bayyana da salon tilawa daban-daban, wanda hakan ne yasa hukumumi a wanann bangaren suke daukar matakan sanya ido da kuma tabbatar da cewa tsari wanda ya dace a wannan bangare.

 

 

3982010

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar masar
captcha