IQNA

Zarif: Jarunta Wajen Yin Sulhu Da Juna Tafi Jarunta A Wajen Yaki

21:22 - July 08, 2021
Lambar Labari: 3486085
Zarif ya ce Iran za ta ci gaba da taimakawa domin ganin an samu sulhu da fahimtar juna a tsakanin dukkanin bangarorin al'ummar Afghanistan.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif  a cikin wata makala da ya saka a shafinsa na twitter a daren jiya, ya bayyana cewa, har kulum Iran tana tare da al’ummar kasar Afghanistan, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da taimaka musu ko bayan ficewar sojojin mamaya a kasar.

A jiya ne aka bude wani zaman taro a birnin Tehran, wanda ya hada manyan jami’an gwamnatin kasar Afghanistan, da kuam jagororin kungiyar Taliban, gami da wakilan wasu bangarori na kasar ta Afghanistan, wanda kuma ministan harkokin wajen kasar ta Iran Muhammad Jawad Zarif ne ya jagoranci zaman taron.

Babbar manufar Iran ta shirya wannan taro wanda ya hada wakilan dukkanin bangarorin al’ummar kasar Afghanistan a Tehran shi ne, samar da hanyoyi na sulhunta bangarorin da suke da sabani, musamman ma gwamnatin kasar da kuma kungiyar Taliban.

Zarif ya ce, al’ummar kasar Afghanistan ne kawai za su iya samar da sulhu da zaman lafiya a kasarsu, ta hanyar fahimtar juna tsakaninsu, da kuma hada kai tsakanin dukkanin bangarori domin yin aiki tare da juna, domin gina kasarsu da kansu, ba tare da yin katsalandan na kasashen ketare ba.

 

 

captcha