Shafin yada labarai na maa News ya bayar da rahoton cewa, duk da matakan da Isra'ila ta dauka, amma fiye da Falastinawa dubu 35 ne suka gudanar da sallar Juma'a a yau a ciki da kuma harabar masallacin aqsa mai alfarma.
Isra'ila ta girke jami'an tsaron yahuwa masu yawan gaske a dukkanin sassa na masalalcin quds, da kuma dukkanin hanyoyin da suke masallacin da ke cikin birnin.
Bayan kammala sallar Juma'a jami'an tsaron yahudawan sun kame wani matashi bafalastine, bayan da ya daga tutar Falastinu a wurin.