IQNA

Tehran (IQNA) wannan shi ne hubbaren Imam Jawad (AS) jikan manzon (SAW) a garin Kazimai na Iraki.

An haifi Imam Jawad (SA) a ranar 10 ga watan Rajab shekara ta 195  hijira kamariyya a birnin Madina, shi da ne ga Imam Aliyu Ridha (AS) dan Imam Kazem (AS) dan Imam Sadiq (AS) dan Imam Baqer (AS) dan Imam Zainul Abidin (AS) dan Imam Hussain (AS) dan Fatima Zahra (AS) diyan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka.