IQNA

Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Kirayi Jakadiyar Slovenia A Tehran

23:03 - July 12, 2021
Lambar Labari: 3486100
Tehran (IQNA) ma'aikatar harkokin wajen Iran ta kirayi jakadiyar kasar Solvenia a Tehran.

Gwamnatin kasar Iran ta yi allawadai da matakin  firai ministan kasar Slovenia na halartar taron kungiyar ‘yan ta’adda masu adawa da jamhuriyar musulunci ta Iran, wacce aka fi sani da MKO.

Ministan harkokin wajen Iran ya kara da cewa dole ne kungiyar tarayyar turai ta bayyana matsayinta dangane da abubuwan da Firai ministan ya fada a taron, don shi ne yake rike da shugabancin kungiyar ta na karba–karba a halin yanzu.

A maida martanin da ya yi, babban jami'i mai kula da siyasar wajen tarayyar turai ya fadawa Zarif kan cewa firai ministan Sloveniya ba ya wakiltar kungiyar tarayyar Turai a taron na kungiyar yan ta’adda masu adawa da JMI wacce aka fi sani da MKO. Kuma maganganun da ya yi a taron ba ra’ayin kungiyar ne dangane da kasar Iran ba.

Banda haka ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, a nan birnin Tehran ta kira jakadiyar Slovenia da ke nan Tehran zuwa ma’aikatar harkokin wajen kasar don bayyana korafinta kan halattar taron na MKO da kuma jawaban da Firaministan kasarta ya yi.

 

 

3983340

 

Abubuwan Da Ya Shafa: jakadiyyar adawa bayyana shugabancin minista
captcha