IQNA

22:53 - July 22, 2021
Lambar Labari: 3486129
Tehran (IQNA) Isra’ila ta fara nuna damuwa game da bangado leken asirin da ake zargin kamfanin NSO na kasar da hannu a ciki.

Isra’ila ta fara nuna damuwa game da bangado leken asirin da ake zargin kamfanin NSO na kasar da hannu a ciki.

A halin da ake ciki dai Isra’ilar ta kafa wani kwamitin bincike domin bin diddigin lamarin, bisa fargabar kada hakan ya janyo mata rikicin diflomatsiyya.

Ministan tsaron kasar Benny Gantz, ya ce sunan nan suna duba batun.

A kwanan nan ne dai aka bankado labarin leken asirin da ake zargin kamfanin Isra'ila mai leken asiri na NSO da kuma Pegasus.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Shugaban kasar Iraki Barham Saleh da na cikin mutane dubu 50 da ake zargin an yi wa leken asiri da manhajar ta Pegasus.

 

3985779

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: