Shafin yada labarai na jaridar Alwafd ya bayar da rahoton cewa, Ibrahim najm mataimakin babban mai bayar da fatawa na kasar Masar ya bayyana cewa, an kammala dukkanin shirye-shiryen gudanar da taron fatawa ta hanyar kafofin sadarwa na zamani.
ya ce a halin yanzu dai wakilan kasashe 85 ne za su halarci taron na kasa da kasa kan fatawa a kafofin sadarwa na zamani da zai gudana a ranakun 2 da kuma 3 ga watan Agusta mai kamawa.
Taron wanda na karawa juna sani ne, zai samu halartar masana daga wadannan kasashe, wadanda za su bayyana mahangarsu dangane da hanyoyin da ya kamata a kyautata lamarin fatawa ta hanyoyi na zamani, domin musulmi su amfana da hakan cikin sauki a duk inda suke a duniya.
Baya ga haka kuma a zaman za a tattauna hanyoyin da suka dace domin fitar da fatawoyi da suke a kan hanya, domin yi wa matasa saiti wadanda akan yaudare su tare da saka su cikin ayyukan ta'addanci da sunan addini.