Kamfanin dillancin labaran kasar Mauritania ya bayar da rahoton cewa, ministan matasa da wasanni da raya al'adu na kasar Mautaniya Sidi Muhammad Wuld Aswidat ya bayyana cewa, an bude wani bangare na kur'ani a gidan rediyo da talabijin na gwamnatin Mauritaniya da ke a babban birnin kasar.
Ya ce yanzu haka an kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata domin aiwatar da wannan shiri, wanda zai kunshi watsa shirye-shirye na kur'ani kai.
Ministan Mautania ya ce, za a rika sanya karatun kur'ani na makarantan kasar bisa tsarin tilawar da aka saba da ita akasar ta Warsh, kamar yadda kuma za a rika koya ilmomin kur'ani da wasu daga cikin hadisan ma'aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka.
Sisi Muhammad Wuld Mukhtar Anbalil babban daraktan hukumar rediyo da talabijin ta kasar Mauritania ya bayyana cewa, wannan shiri zai taimaka matuka musamman ga matasa masu sha'awar lamurran kur'ani.