Mohsen Isma'ili malamin jami'ar Tehran ya bayyana cewa, abin da ya faru da zuriyar manzon Allah (SAW) na tozarci da kisan kiyashin da masu kiran kansu musulmi suka yi musu shi ne abu mafi muni da ya faru shekaru bayan wafatin manzon rahma.
Ya bayyana hakan ne a bayanin da yake gabatarwa wanda ake watsawa ta hanyar yanar gizo wanda masu bibiyar bayanan a cikin harshen farisanci sukan tarjama su zuwa wasu harsuna domin amfanin al'ummar musulmi.