IQNA

Bankin Musulunci Na Bunkasa Ayyukan Ci Gaba Zai Saka Hannayen Jari A Najeriya

21:05 - August 13, 2021
Lambar Labari: 3486198
Tehran (IQNA) bankin musulunci mai kula da bunkasa ayyukan ci gaba zai saka hannayen jari a Najeriya.

Rahotanni daga Najeriya na cewa, bankin musulunci mai kula da bunkasa ayyukan ci gaba zai saka hannayen jari a kasar.

Malam Ibrahim Garba Muhamamd, babban jami'in hukumar bunkasa ayyukan noma da kiwo a jihar Kano KSADP ya bayyana cewa, wannan shiri zai shafi ayyuka da dama a wannan fagea  cikin jihar Kano.

Ya ce bankin zai saka kuadde masu tarin yawa a jihar Kano domin ganin an bunkasa ayyuka da suka shafi kiwo da kuma noma, wanda hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga dubban matasa da kuam magance matsalar karancin abinci.

 

3990372

 

 

 

captcha