Kamar sauran birane da dama na kasashen turai, a birnin Landan na kasar Burtaniya ma an gudanar da taron juyayin Ashura domin tunawa da abin ya faru da Imam Hussain (AS) da zuriyar manzon Allah (SAW) da suke tare shi a wannan rana, na cin zarafi da kisan gilla da aka yi musu bisa zalunci.
Sheikh Fadil Maliki na daga cikin malaman da suka gabatar da jawabi a gaban mahalrta wannan taro, inda ya yi bayani kan abin da ya faru, da kuma fitar da darussa da ya kamata musulmi su dauka daga waki'ar Ashura.
An fara gudanar da gangami ne daga hyde Park da ke tsakiyar birnin Landan, inda aka yi jerin gwano har zuwa babban titin Oxford.