IQNA

Masar Ta Rufe Mashigar Rafah Domin Yin Matsin Lamba A Kan Kungiyar Hamas

19:10 - August 23, 2021
Lambar Labari: 3486232
Tehran (IQNA) Masar ta sanar da rufe mashigar Rafah wadda ta hada iyakokin kasar da yankin zirin Gaza na Falastinu.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar Masar sun sanar da cewa, rufe wannan mashigar yana da alaka ne da shiga tsakanin da Kasar Masar take yi tsakanin Isra’ila da kuma kungiyar Hamas.

Haka nan kuma wani daga cikin jami’an gwamnatin kasar ta Masar ya ce, an dauki wannan matakin ne da nufin yin matsin lamba a kan kungiyar Hamas dangane da batun dakatar da bude wuta tsakaninta da Isra’ila, kamar yadda kuma ya bayyana cewa ba a san har zuwa wane lokaci ne mashigar ta Rafah za ta ci gaba da kasancewa a rufe ba.

Mashigar Rafah dai ita ce babbar mashigar da ake shigar da kayayyakin bukatar rayuwa ga al’ummar yankin Zirin Gaza, wanda Falastinawa mazauna yankin zirin Gaza suke yin amfani da ita domin ci gaba da rayuwa.

Gwamnatin kasar Masar tana yin amfani da mashigar Rafah domin yin matsin lamba akan Falastinawa musamman ma kungiyoyin gwagwarmaya na yankin zirin Gaza, inda ta kan rufe wannan mashiga a duk lokacin da ta ga dama, domin yin matsin lamba a kansu domin su amince da wasu bukatu na Isra’ila ko kuma wasu kasashen na daban.

 

3992663

 

 

 

 

captcha