IQNA

Matshi Mai Baiwar Karatun Kur'ani Da Salo Na Shahararrun Makaranta 10 Na Duniya

17:40 - August 27, 2021
Lambar Labari: 3486244
Tehran (IQNA) matashi dan kasar Masar da Allah ya yi masa baiwa ta karatun kur'ani da salo na fitattun makaranta 10 na duniya.

Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, Muhammad Khairi Sa'adallah matashi mai shekaru 19 da ke karatun jami'a, daga garin gardaqah na kasar Masar, wanda Allah ya yi masa baiwa ta karatun kur'ani da salo na fitattun makaranta 10 na duniya ta hanya mai ban mamaki.

Wannan matashi mai baiwa ta musamman wajen karatun kur'ani ya bayyana cewa, ya samu tarbiyya ta kur'ani ne a gaban mahaifansa.

Daga bisani kuma ya ci gaba da karatun kur'ani a makarantar islmiyya, kamar yadda kuma yake kokarin yin tilawa da sauti mai kyau domin tabbatar da cewa yana aiki da hukuncin karatu na tajwidi.

Baya ga haka kuma ya sanya ma kansa bin salon karatu na manyan makaranta irin su Sheikh Kalil Husari da makanatansu, domin hakan ya kara ba shi karfin gwiwa wajen yin karatun yadda ya kamata.

Duk da cewa yana karatun boko, amma wannan bai hana shi ci gaba da yin karatun kur'ani ba, kuma a halin yanzu yana da shekaru goma sha tara kuma yana karatun jami'a.

Daga karshe ya yi godiya ga Allah kan wannan baiwa, sannan kuma ya bayyana fatansa na ganin ya kammala hardar kur'ani nan da wani dan lokaci kadan.

 

 

3992837

 

Abubuwan Da Ya Shafa: matashi
captcha