Manyan kungiyoyin gwagwarmayar Falastinu Hamas da kuma Jihadul Islami sun zargi shugaban falastinawa Mahmud Abbas Abu Mazin da cin amanar al'ummar falastinu, bayan ganawa da ya yi da manyan jami'an gwamnatin yahudawan isra'ila a asirce.
Kafofin yada labarai daga Isra’ila sun rawaito wata ganawa da akayi tsakanin shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas da kuma ministan tsaron Isra’ila Benny Gantz a birnin Ramallah.
Wannan dai ita ce ganawa irinta ta farko cikin shekaru goma a wannan matsayi tsakanin Isra’ila da Falasdinu.
Yayin ganawar da aka shafe sa’o’i biyu da rabi ana gudanar da ita, da kuma ganawa ta kud-da-kud ta muntina 40, bangarorin sun tattauna kan batutuwan da suka shafi inganta tsaro da tattalin arziki a Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza, kamar yadda Isra’ila ta ambato a cikin wata sanarwa.
Haka kuma za’a aiwatar da wani sassaci, sannan bangarorin biyu sun yi alkawarin ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu.
Ganawar dai ta zo ne ‘yan sa’o’I kadan bayan ziyarar da firayi ministan Isra’ila Naftali Bennett, ya kai a birnin Washington, inda ya gana da shugaban Amurka Joe Biden.