IQNA

An Samar Da Wurin Salla Ga Masu Larura Ta Musamman A Masallacin Haramin Makka A Lokutan Umrah

17:31 - August 31, 2021
Lambar Labari: 3486256
Tehran (IQNA) an samar da wurin salla ga masu larura ta musamman a cikin masallacin haramin Makka mai alfarma a lokutan Umrah.

Hukumar da ke kula da lamurran masallacin haramin Makka da masallacin manzo da ke Madina ta sanar da samar da wurin salla ga masu larura ta musamman a cikin masallatan biyu masu alfarma a lokutan Umrah.

Amjad Bin Ayid Alhazimi shugaban ma'aikata masu gudanar da hidima a cikin haramomin biyu ya bayyana cewa, wadanda suke da larurori kamar guragu, ko makafi da makamantansu ne kawai za su iya yin amfani da wurin.

Ya kara da cewa, samar da wurin zai taimaka matuka ga masu larurori na musamman wajen gudanar da ayyukansu na ibada a lokutan umrah ba tare da wata matsala ba.

Ya kammala da cewa shugaban hukumar ne da kansa ya bayar da umarinin samar da wannan wuri, da kuma samar da abubuwa na kiwon lafiya da hana yaduwar cutar corona gare su, kamar takunkumin rufe fuska da kuma abubuwan fesawa na kashe kwayoyin cuta.

3994138

 

captcha